A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza daga birnin Tehran, Ayatullah Hashemi-Olya, a ranar Laraba yayin wani zama na darasin tarbiyya (Akhlak) da aka gudanar na musamman domin dalibai, ya yi bayani kan muhimmancin talauci, wadata, da kuma tasirin ayyukan dan adam. Ya jaddada rawar da godiya, bauta, da kiyaye adalcin zamantakewa suke takawa wajen samun albarkar Ubangiji.
Ya bayyana cewa: "Dole ne dan adam ya nemi tsari ga Allah, kuma ya kalli dukkan ni'imomi da iyawarsa ta mahangar Ubangiji. Talauci da matsalar kudi na mutum ba wai alamar rauni ba ne, a'a, dama ce ta samun kusanci ga Allah da kuma ci gaban ruhi da dabi'u."
Ayatullah Hashemi-Olya ya kara da cewa dukkan iyawa, ilimi, sani, da karfin mutane suna kasancewa ne da izinin Allah kuma daga gare Shi suke, babu wani mutum da zai iya yin wani abu shi kadai sai da nufin Allah Madaukakin Sarki. Ya ambato fadin Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ina alfahari da kasancewa mabuqaci (talaka), domin dukkan bayin Allah mabuqata ne zuwa ga Allah, kuma duk abin da suke da shi daga Allah yake."
Wanda ya assasa makarantar ta Qa'im ya jaddada cewa: "Talauci da wadata duka kayan aikin jarabawar Allah ne. Mutum kada ya fita daga tafarkin bauta da godiya ko yana cikin talauci ne ko a wadace. Hatta taimakon da mutum yake ba dan uwansa ba zai yiwu ba sai da izinin Allah. Kowane digo na ruwan sama, kowace ganye da yake faduwa daga bishiya, da kowane taimako na dan adam, duk suna faruwa ne da izinin Allah a matsayin hanyar kwararar falalar Ubangiji."
Ya ci gaba da cewa: "Lokacin da Allah Ya ba mutum ikon taimakon wani, to ku yi maza ku yi amfani da wannan damar, kuma ku sani cewa wannan ma jarabawa ce ga bangarorin biyu; ga talaka da kuma mai kudin. Taimaka wa mabuƙata da kyautata wa talakawa yana tafiya tare da samun albarka a duniya da lada a lahira."
Ayatullah Hashemi-Olya ya ja hankali kan tasirin ayyukan mutum inda ya ce: "Ayyukan mutum ba kawai a rayuwarsa suke tsayawa ba, suna shafar iyalinsa, 'ya'yansa, da ma al'umma baki daya. Kowane aiki da muke yi, tun daga bauta har zuwa dabi'unmu a cikin jama'a, yana da tasiri da albarka. Rayuwar malamai da manyan bayin Allah misali ne bayyananne na wannan gaskiyar; ayyukansu da bautarsu sun yi tasiri ba ga kansu kadai ba, har ma ga al'umma."
Ya kara da cewa: "Gidajen da ake bauta da ambaton Allah a cikinsu, tare da yin sallar dare da karatun Alkur'ani, suna da albarka ta musamman. Barin wadannan ayyuka da gafala daga al'amuran ruhi yana rage albarkar rayuwa har ma yana gajarta rayuwar mutum."
Malamin na Hauza ya yi ishara da matsayin talakawa a koyarwar addini, inda ya ce: "Ku kulla abota da talakawa, ku kyautata musu kuma ku taimaka musu, domin Allah Madaukakin Sarki yana da wata kulawa ta musamman ga talakawa a ranar kiyama, har ma zai yi mu'amala da su kamar yadda mutum yake ba da hakuri (ga wanda aka zalunta). Kaskantar da mabuƙata yana sanya mutum rashi ga albarkacin Ubangiji, kuma a ranar kiyama sakamakon wannan dabi'a zai fito fili."
Ya nuna cewa: "Kaskantar da talakawa ba wai kawai dabi'a ce mara kyau ba, a'a, yana iya samun babban tasiri a duniya da lahira. A koyarwar addini an fadi cewa wanda ya kaskantar da mabuƙaci ko talaka, hanyar shiga Aljanna za ta toshe a gare shi, sannan har ayyukansa na baya za a sake duba su a ranar kiyama."
A ci gaba da bayanin sa, Ayatullah Hashemi-Olya ya taba mahimmancin hakuri da dogara ga Allah (Tawakkul) yayin fuskantar matsalolin rayuwa: "Rayuwa a cikin tsananin matsaloli da kunci jarabawa ce ta Ubangiji. Kowane matashi, mace, namiji, ko iyali da ke kokawa da matsaloli, a zahiri suna fuskantar jarabawar Allah. Mutum a wannan hali ya rike bauta da komawa zuwa ga Allah, sannan ya guji zunubai da ayyukan kuskure."
Malamin na Hauza ya kara da cewa: "Tsanani da matsaloli da kuma karancin abubuwan more rayuwa, dama ce mai kyau ga dan adam domin ya nuna godiyarsa ga Allah, kuma kada ya kauce daga tafarkin Ubangiji. Kowane aiki da mutum yake yi domin Allah, yana da tasiri mai girma fiye da yadda ake tunani, kuma yana iya kawo albarka ga rayuwar kansa da ma na mutanen da suke kewaye da shi."
Yayin da yake jaddada mahimmancin yin godiya, ya bayyana cewa: "Muminin gaskiya shi ne wanda yake kallon dukkan al’amuran rayuwarsa a matsayin abubuwa daga wajen Allah, kuma ya kasance mai godiya a kowane hali; walau a lokacin lafiya ko rashin lafiya, a lokacin wadata ko na talauci. Ayyukan dan adam jarabawa ce daga Ubangiji, kuma kowane taku da yake yi, yana karkashin idon Allah (kulawar Allah) ne."
Ayatullah Hashemi-Olya a karshe, ya jaddada cewa: "Dole ne mutum ya dogara ga Allah a kowane hali, kuma ta hanyar godiya da ayyuka na gari, ya kiyaye hanyar bauta. Kowane aiki da aka yi da niyyar neman yardar Allah, zai tafi tare da albarka a duniya da lahira, kuma zai sa mutum ya yi nasara a jarabawar Ubangiji."
Your Comment